Take a fresh look at your lifestyle.

Lardin Manitoba Ta Kanada Zata Tuna Da Ranar ‘Yancin Najeriya

179

Gwamnatin lardin Manitoba na kasar Kanada ta gabatar da wani kudirin doka don tunawa da ranar ‘yancin kai na Najeriya da kuma murnar al’ummar Najeriyar da ke lardin.

Ministan lafiya da tsofaffi da kuma na dogon lokaci, Uzoma Asagwara ne ya gabatar da kudirin a gaban majalisar dokoki.

Kudirin yana da nufin wayar da kan al’ummar Najeriya kan ranar ‘yancin kai a tsakanin dukkan ‘yan kabilar Manitoban.

Uzoma Asagwara, dan Najeriya na farko kuma daya tilo a majalisar dokokin Manitoba, ya bayar da shawarar ayyana ranar 1 ga Oktoba a matsayin bikin ranar ‘yancin Najeriya.

Wannan ranar tana da matukar muhimmanci. A yau, muna tunanin dukan dattawa a cikin al’umma da suka sadaukar domin al’ummai masu zuwa su bunƙasa a Manitoba,

“Wannan kudiri ya daukaka duk wadanda ke cikin al’umma da suka bayar da shawarar don mu kasance a inda muke a yau da kuma zaburar da al’ummomi masu zuwa suyi alfahari da su.” Asagwarasaid.

Manitoba ita ce lardi na biyar mafi yawan jama’a a Kanada, tare da ‘yan Najeriya kusan 7000 da ke zaune a can.

Asagwara ya yi imanin amincewa da ranar ‘yancin Najeriya a hukumance ta hanyar wannan doka zai sa ‘yan Najeriya a Manitoba su ji kima.

Asagwara ya kara da cewa, kudirin dokar zai karfafawa daukacin al’ummar Manitoba kwarin gwiwar sanin irin gwagwarmayar da ‘yan Najeriya suka sha da kuma irin gagarumar gudunmawar da suke bayarwa a lardin.

Wannan kudirin doka zai haifar da wayar da kan jama’a ga duk Manitobans don sanin ranar ‘yancin kan Najeriya, abin da ‘yan Najeriya suka ci nasara da kuma gagarumar gudunmawar da suka bayar ga lardin mu baki daya,” in ji Asagwara.

An haife shi kuma ya girma a Kanada, Uzoma Asagwara ma’aikaciyar jinya ce mai rijista, tsohon ɗan wasan ƙwallon kwando kuma wakilin gundumar zaɓe ta Union Station a Majalisar Dokoki ta Manitoba tun daga 2019.

Asagwara memba ne na Manitoba New Democratic Party.

 

Comments are closed.