Take a fresh look at your lifestyle.

An Kama Mutum Tara Bayan Harin Da Aka Kai A Ofishin ‘Yan Sanda Na Paris

189

Shugaban ‘Yan Sandan Birnin Paris ya bayyana cewa, an kama mutane tara bayan da aka kai hari a wani ofishin ‘yan sanda da ke unguwar La Courneuve a yammacin ranar Lahadin da ta gabata sakamakon arangamar da aka yi tsakanin matasa da jami’an ‘yan sanda.

Rikicin dai ya biyo bayan mutuwar wani matashi a makon da ya gabata wanda ya kasa tsayar da babur dinsa bayan da ‘yan sanda suka umarce shi da ya yi hakan.

Laurent Nunez ya ce “An kama mutane tara, wadanda ba su da muhimmanci.”

“Karfafa ‘yan sanda ya dawo da tsari da tsaro cikin sauri,” in ji shi.

Batun tsaro na da matukar muhimmanci ga mahukuntan Faransa tare da gasar Olympics da za a fara a ranar 26 ga watan Yuli.

An lalata wasu wuraren wasannin Olympics na birnin Paris yayin tarzoma a lokacin bazarar shekarar 2023, sakamakon harbin da ‘yan sanda suka yi wa wani matashi dan asalin Afirka ta Arewa.

 

Comments are closed.