Take a fresh look at your lifestyle.

An Rantsar da Sanata Saliu Mustapha A Matsayin Wakili A Majalisar Hadin Kan Yanmajalisun Dokokin Kasashen Afrika

Abdulkarim Rabiu, Abuja.

112

An rantsar da Sanata Saliu Mustapha, jagoran tawagar Najeriya zuwa babban zama na musamman na majalisar hadin kan kasashen Afrika karo na 6 da ya gudana a birnin Midrand na kasar Afirka ta Kudu a matsayin dan majalisar.

Sanata Mustapha ya karbi rantsuwar ne tare da sauran wakilan Najeriya a wajen bude taron biyo bayan zabinsa da shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ya yi.

Sanatan mai wakiltar Kwara ta tsakiya wanda ya jagorancinsa na tawagar Najeriya ke tabbatar da zurfin fahimtarsa ​​kan al’amuran Afirka, ana sa ran zai yi amfani da kwarewarsa a fannin diflomasiyya da tattaunawa wajen bada gudunwa kan sabon mukaminsa.

Majalisar Hadin Kan Yan majalisun Dokokin kasashen Africa (PAP) ita ce majalisar dokoki ta Tarayyar Afirka (AU) kuma wani dandali ne da aka baiwa jama’a daga dukkan kasashen Afirka su shiga a dama da su wajen tattaunawa da yanke shawara kan kalubalen ci gaban tattalin arziki da hadin kan kasashen nahiyar.

 

Abdulkarim

Comments are closed.