Take a fresh look at your lifestyle.

JIHAR JIGAWA TA ZAMA JAGORA A AYYUKAN GONA-MINISTA

Yusuf Bala,Kano.

70

Jihar Jigawa Arewa maso Yammacin Najeriya ta zama jagora a wajen samar da albarkatun gona a cewar ministan yada labarai da wayar da kan al’umma a Najeriya  Muhammad Idris.

 

Ministan ya bayyana haka ne a fadar gwamnatin jihar ta Jigawa da ke Dutse a ziyarar aiki da ya kai jihar Jigawa. Ministan yace hakan ya biyo bayan yadda gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Umar Namadi ta mayar da hankali da aiki tukuru don tabbatar da ganin jihar na samar da albarkatun gonar cikin kokarin da kasar ta sa a gaba na samun damar dogara da kai a fannin na samar da abinci.

 

A cewar ministan sun isa jihar Jigawa ne tare da wakilai daga fadar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubiu da shugabannin kafafen yada labarai don isar da sakon shugaban kasa ga ‘yan Najeriya da irin ayyukan da gwamnati ta sa a gaba don samarwa ‘yan Najeriya saukin rayuwa. Yace “babu shakka ‘yan Najeriya na fuskantar kalubale musamman tun bayan cire tallafin manfetir saboda haka ne ma gwamnati ta zage damtse da hada kai da gwamnatin jihohi domin samar da mafita a gare su wacce za ta zama mai dorewa”.

 

“Muna sane da cewa ba da dadewa bane gwamnatin jihar ta Jigawa ta ware sama da Naira miliyan dubu don samar da kayayyakin tallafi ga ma’aikata don su rage radadi.  Jigawa ta kasance a gaba wajen ganin gwamnatin ta cika burinta na wadata kasa da abinci wanda ke zama daya cikin ginshikai takwas da gwamnatin Shugaba Tinubu ta sa a gaba.Kan haka ne gwamnati a watan Nuwamba, 2023 ta zo Jigawa karkashin shirin gwamnatin tarayya bisa daukar nauyin Bankin raya Kasashen Afurka  ta kaddamar da aikin noman rani da zai samar da alkama da shinkafa da masara da dawa  da waken soya aikin da ake ci gaba da yinsa har kawo yanzu”

 

Ministan  yayi amfani da wannan dama wajen sake bayyana manyan ajandodi da ma’aikatar yada labarai da wayar da kan al’umma tasa a gaba mai ajanda  guda biyar da suka hadar da;1-Tabbatar da ganin al’umma sun aminta da ababen da kafafan yada labarai na gwamnati ke yadawa  2- Bayyana ayyuka da tsare-tsare na Gwamnatin Tarayya da ke zama nagartattu 3-Sabunta al’amuran da suka shafi kishin kasa tsakanin gwamnati da al’ummarta 4- Tabbatar da tafiya da ci gaban fasahar zamani  da kirkira a bangaren harkokin samar da bayanai na gwamnatin tarayya 5-Samar da kyakkyawan yanayi da tsare-tsare da kafafan yada labarai za su yi aikinsu. Ministan yace a shirye suke wajen yada abubuwan ci gaba da gwamnatin ta Jigawa take yi.

 

A nashi martini gwamnan na jihar ta Jigawa Umar Namadi yace jihar ta Jigawa ta dukufa wajen cimma muradin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ajandarsa ta “Sabunta fata ga ‘yan Najeriya” inda a bangaren na aikin gona take zuwa da sabbin tsare-tsare da suka hadar da inganta ayyukan malaman gona da daukar wasu 1400 sabbi, irin wannan ne ma ya sa jihar ta zama ta daya wajen samar da Zobo a Najeriya, baya ga saura kan haka ne ma jihar da hadin gwiwa fanni mai zaman kansa ta samar da wata cibiya a Maigatari  ta alkinta Zobo da ake samarwa, wanda daga nan za a iya daukarsa kai tsaye zuwa kasashen ketare da a cewar gwamnan Zobo da ridi su ke bada kaso mafi tsoka na abin da jawowa Najeriya kudaden shiga, Wanda bisa kiyasi za a iya cewa jihar na samarwa  kasar kaso 75 cikin dari na kudaden shiga a fannin da ba na manfetir ba.

 

Yace aikin Fadama da gwamnatin tarayya ke yi da Bankin Duniya a jihar ya samar da sauyi a rayuwar al’ummar jihar ta Jigawa maza da mata wanda da harkar zobo kadai ya sauya rayuwar dubban al’umma ta hanyar samun kudaden shiga da rage talauci a tsakanin al’umma.

 

Ministan dai da tawagarsa sun zagaya wurare da dama da suka hadar da fadar sarkin Dutse da manyan gonaki da ake noman rani a garuruwan Auyo da Ringim don gani da idanu, da a cewar ministan lokacin aiki da za a zauna kawai a Abuja da takardu kadai ya kare.

 

 

Yusuf Bala.

 

 

 

 

 

Comments are closed.