Take a fresh look at your lifestyle.

Rundunar Sojin Najeriya Ta Kaddamar Da Ayyukan Ci Gaba Ga Al’ummar Jihar Sokoto

Shehu Salman, Sokoto

192

Babban hafsan runduna ta sojin ƙasa na Najeriya wato COAS Lt. Gen. Taoreed Abiodun Lagbaja ya ce sun kaddamar da ayyukan ne domin amfanin al’ummar jihar Sokoto bisa irin goyon baya da suke baiwa jami’ansu a daidai lokacin da suke gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya da kuma yaƙi da masu sata da garkuwa da mutane domin karbar kuɗin fansa.

Kwamandan rundunar sojin ta 8 Maj. Gen. Godwin Michael Mutkut shi ne ya wakilci COAS yayin ƙaddamar da ayyukan da suka haɗa da samar da ruwan sha ta hanyar gina rijiyoyin burtsatse, rarraba magunguna ga asibitoci, tsaftace muhalli, tallafawa marasa ƙarfi da dai sauransu. A cewar babban hafsan wannan somin taɓi ne bisa tsaretsaren da rundunar ta yi na tallafawa al’ummar jihar Sokoto.

Ƙoƙarin na rundunar sojin har ila yau wani ɓangare ne na yauƙaƙa dangantaka tsakanin soji da farar hula wato civil-military relations a turance wanda kwamanda mai kula da ɓangaren Maj. Gen. Nosakhare Ugbo ya ƙara da cewa rundunar tasu na gudanar da irin wadannan ayyukan da nufin kyautata rayuwar al’ummar da take aiki cikinsu a matsayin tukuici dangane da goyon baya da su ke samu daga garesu.

Daga karshe, babban hafsan ya buƙaci al’ummar jihar da su kwantar da hankullansu yayin da rundunar tasu ke ƙoƙarin fatattakar dukkanin ɓata gari da ke ƙoƙarin tada zaune tsaye a faɗin jihar.

Abdulkarim Rabiu

Comments are closed.