Take a fresh look at your lifestyle.

Tsohon kakakin Majalisar Jihar Kuros Riba, Lebo Ya Fice Daga PDP

58

Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kuros Riba, Mista John Lebo ya yi murabus daga mukamin shi na Jam’iyyar PDP.

 

Lebo wanda shi ne kakakin majalisa ta 8, ya bayyana murabus din nasa ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun sa wacce aka rabawa manema labarai a Calabar ranar Lahadi.

 

A cikin sanarwar mai dauke da kwanan watan 10 ga watan Mayu, kuma aka mika wa shugaban jam’iyyar PDP, Aadama Ward, karamar hukumar Abi, Lebo bai bayar da wani bayani kan murabus din nasa ba.

 

“Ina so in sanar da murabus na na zama dan jam’iyyar PDP a dukkan matakai.

 

“Na yaba da dama da tsarin da jam’iyyar ta ba ni a cikin ‘yan shekarun nan. Ina yi muku fatan alheri,” sanarwar ta karanta cikin sassa.

 

Haka kuma tsohon shugaban majalisar bai ambaci yunkurinsa na gaba na siyasa ba bayan ficewa daga jam’iyyar PDP.

 

NAN/Ladan Nasidi.

Comments are closed.