Take a fresh look at your lifestyle.

Kakakin Majalisar Wakilai Ya Nada Hon Chede A Matsayin Jakada A Ofishin Jam’iyyar APC

Abdulkarim Rabiu, Abuja.

79

Kakakin majalisar wakilai Dr Abbas Tajuddeen, ya amince da nadin tsohon dan majalisar wakilai Alhaji Garba Chede a matsayin jami’in hulda a tsakainin Majalisar Wakilai da Sakatariyat jam’iyyar All Progressives Congress APC ta kasa .

A cikin wata sanarwa da shugaban ma’aikatan ofishin kakakin Majalisar Wakilai, Farfesa Jake Dan-Azumi ya fitar, ta ce wanda aka nada shi ne zai kula da dukkan harkokin sadarwa tsakanin majalisar wakilai da sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa.

Kakakin majalisar wanda ya tabbatar wa sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa Karin gwaiwar da yake da shi a kan sabon wanda aka nada mukamin, ya bukace su da su ba shi dukkan goyon bayan da ya dace domin ya samu damar gudanar da aikinsa yadda ya kamata.

Da yake zantawa da manema labarai a kan sabon nadin Alhaji Garba Chede, ya gode wa shugaban majalisar da ya ba shi damar yin aiki a wannan matsayi.

Alhaji Garba Chede, ya kuma yi alkawarin yin amfani da sabon ofishi wajen inganta kyakkyawar alakar aiki tsakanin majalisar da sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa domin samun nasarar gwamnati mai ci a karkashin shugaba Tinubu da ma ta kasa baki daya.

Kafin Nadin nashi Alhaji Garba Chede, tsohon dan majalisar wakilai ne daga mazabar Balli-Gassol a jihar Taraba a majalisa ta takwas da tara.

Abdulkarim Rabiu

Comments are closed.