Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnati Ta Amince Da Biliyan 66 Ga Ayyuka A FCT

32

Majalisar zartaswa ta tarayya ta amince da sama da Naira biliyan 66 domin gudanar da ayyuka a babban birnin tarayya (FCT).

 

Ministar kasa ta babban birnin tarayya, Mariya Mahmud ce ta bayyana hakan ga manema labarai a fadar shugaban kasa bayan taron majalisar da shugaban kasa Bola Tinubu ya jagoranta a Villa da ke Abuja.

 

Ministan ya ce amincewar farko ita ce bayar da kwangilar da ta kai Naira biliyan 51.03 ga Planet Project Limited don gina tashar bas da sauran kayayyakin sufuri a cikin babban birnin tarayya Abuja.

 

Har ila yau, ta ce an amince da bayar da kwangilar Naira biliyan 7.26 ga Visible Construction Limited don gina Kotun Daukaka Kara na sashin Abuja.

 

Mahmud ya ce amincewa na uku shi ne na samar da ayyukan tsaro da kuma kula da na’urorin adana fitilun titunan da ke kan titin fadar shugaban kasa da kuma kofar Villa 8 a babban birnin tarayya. Wannan kwangilar da ta kai Naira miliyan 412.35, an bayar da ita ne ga kamfanin Meshia Contract People Limited.

 

Ministan ya kuma bayyana cewa an amince da kwangilar gyaran hanyar Koita-Igbu a karamar hukumar Kwali Naira biliyan 7.6 sannan an ba da kwangilar hanyar ga kamfanin El Emad Nigeria Limited.

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.