Take a fresh look at your lifestyle.

Afirka Ta Kudu Ta Kare Ƙoƙarin Ceto A Ginin Da Ya Ruguje

146

An kammala aikin ceto da dawo da martaba a wurin da wani gini ya ruguje a George, na Afirka ta Kudu.

 

Bayan kwashe kwanaki 12 ana kokarin, an tabbatar da mutuwar mutane 33, yayin da 19 ba a gansu ba.

 

A ranar Juma’a ne dai karamar hukumar da ke lardin Western Cape ta sanar da kawo karshen aikin ceton.

 

Ministan kula da muhalli da tsare-tsare na lardin ya ce a ranar Juma’a mutane 62 ne a wurin ginin a lokacin da rugujewar ta afku a ranar 6 ga watan Mayu.

 

Anton Bredell ya ce “Na yi matukar farin ciki da cewa za mu iya sake duba adadin mutanen da ke wurin daga 81 zuwa 62, saboda hakan yana nufin karancin iyalai ne ke bakin ciki a yau,” in ji Anton Bredell.

 

Ya kara da cewa mutane 10 har yanzu suna kwance a asibiti, kuma mutane 19 ko dai an sallame su ko kuma an basu jinya a wurin.

 

Daga cikin mutane 34 da aka yi nasarar ceto, 5 sun mutu ne a asibiti.

 

Yawancin wadanda abin ya shafa dai ma’aikata ne daga kasashen waje da suka hada da Zimbabwe da Malawi.

 

Yanzu dai za a mika ginin ga ma’aikatar ayyuka da kwadago ta kasa domin gudanar da bincike kan rugujewar ginin.

 

Aikin ceton ya ga fiye da ton 6,000 na baraguzan gine-gine da aka kwashe yayin da masu aikin ceto.

 

A watan Yuli ko Agusta ne ya kamata a kammala ginin bene mai hawa biyar a gabar tekun kudancin kasar.

 

 

Africanews/Ladan Nasidi.

Comments are closed.