Take a fresh look at your lifestyle.

Hukumar Ta Yaba Wa Gwamnan Jahar Sokoto Akan Raba Kudi Ga Manyan Asibitoci

494

Babban Daraktan Hukumar Kula da Ayyukan Asibitin Jihar Sakkwato, Dokta Bello Abubakar Almustapha, ya yaba wa Gwamna Ahmed Aliyu bisa sake dawo da rabon kudi ga manyan asibitoci daban-daban na kananan hukumomi 23 na jihar.

 

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin jihar Sokoto ta baiwa mata da matasa 100 tallafi

 

Dokta Almustapha ya yi wannan yabon ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke jihar Sakkwato.

 

Ya ce kudaden da aka ware wa asibitocin na daga cikin alkawuran yakin neman zabe da Gwamnan ya yi na inganta yanayin aiki ga ma’aikatan lafiya.

 

” Gwamnatin da ta shude ta yi watsi da kudaden alawus-alawus na asibitocin tsawon shekaru, yanzu haka Gwamna Aliyu ya yi alkawarin sake dawo da shi a lokacin yakin neman zabe. A yanzu alkawarin ya cika kuma an inganta ayyukan hidima musamman tsaftar asibitoci daban-daban,” inji shi.

 

Ya kuma yi kira ga ma’aikata da su mayar da martani ta hanyar tabbatar da cewa sun jajirce wajen gudanar da ayyukansu tare da kara himma ga wannan sana’a domin samar da ingantacciyar hidima ga al’ummar jihar.

 

Dokta Almustapha ya kara nanata shirin Gwamna Aliyu na gyarawa tare da inganta duk wani babban asibitin da ke fadin kananan hukumomi 23 na jihar.

 

Babban Daraktan ya lura cewa gwamnati mai ci za ta ci gaba da ba da fifikon jin dadin dukkan ma’aikatan lafiya don samun ci gaba mai dorewa a jihar.

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.