An Kaddamar Da Shirin Horas Da Malaman Makaranta Dubu Goma Sabbin Dabarun Koyarwa A jihar Katsina
Kamilu Lawal,Katsina.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya kaddamar da wani shiri na musamman domin bada horo ga malaman makaranta dubu goma a fadin jihar
Gwamnan Radda ya kaddamar da shirin ne a babban dakin taro na sakatariyar jihar dake birnin Katsina
Dukkannin sabbin Malamai dubu bakwai da dari ukku da ashirin da biyar (7,325) da gwamnan ya dauka aiki a farkon shekarar nan ta 2024 zasu amfana da shirin horaswar yayin da ragowar malaman an dauko su ne daga cikin wadanda suka dade suna koyarwar a makarantun jihar daban daban
Dukkanin mahalartan da zasu amfana da shirin za’a koyar da su dabarun koyarwa daidai da zamanin da muke ciki na karni na ashirin daya wato 21th Centuary Teaching Methodologies
A jawabin sa wajen kaddamar da shirin, gwamnan jihar, Malam Dikko Radda ya jaddada kudurin gwamnatin sa wajen tabbatar da cewa malaman makaranta na da kwarewar da zasu ilmantar da yara ilmi mai inganci wanda zai bude masu kyakkyawan tunanin ciyar da kasa gaba
Ya bayyana malaman makaranta a matsayin ginshikin cigaban kowace al’umma
“Shigo da dabarun koyarwa daidai da zamani ga malaman mu, wata mafita ce da zata basu damar kawo wani sabon sauyi ga tsarin koyarwa a makarantun mu, muna gogad dasu ne da hanyoyin da zasu rika kyankyashe mana dalibai wadanda zasu cimma burin da kasa ke bukata kuma tayi alfahari da su a wanna zamani da muke ciki”, Gwamna Radda ya bayyana.
Kamilu Lawal.
Comments are closed.