Take a fresh look at your lifestyle.

TSN Ta Bukaci Zababbun Sanatoci Su Zabi Shugaba Mai Hangen Nesa

Abdulkarim Rabiu, Abuja

0 127

Shugaban gamayyar kungiyoyin dake goyan bayan Zabben Shugaban kasa ta TSN da Amalgamated Conference of all support Groups Injiniya Kailani Muhammad ya bukaci zababbun Sanatoci da su zama masu hadin kai kuma su jajirce wajen zaben sahihin shugaba wanda zai ja ragamar shugabancin majalisar dattawa.

Injiniya Kailani Muhammad ya yi wannan kira ne a lokacin da ya ke maraba da zababbun Sanatoci a wajen liyafar cin abinci ta musamman domin karrama zababbun Sanatoci 109 na Majalisar Dokokin Najeriya ta 10.

Injiniya Kailani ya kara da cewa idan har ana son ciyar da Najeriya gaba, ya kamata zababbun sanatocin da su hada kai wajen zabar shugaban majalisar dattawa mai hangen nesa, mai manufofi irin su Abdulazeez Yari don ganin an amfana da romon dimokuradiyya a kowane lungu da sako na kasarmu tare da cimma burin da ya kamata na jam’iyyar All Progressives Congress APC.

A cewar Shugaban na kungiyar ta TSN and Amalgamated Conference na dukkan kungiyoyin goyon bayan ya ce majalisar dattawa ta 10 tana bukatar mutane irin su Abdulazeez Yari wanda shi ne mai nasara kuma mai hada kai, domin wannan gwamnati ta cimma manufofinta.

Har ila yau ya taya ‘yan Najeriya murnar samun Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Shettima a matsayin shugabannin Najeriya a bangaren zartarwa da kuma samun Sanata Abdulazeez Yari a matsayin shugaban majalisar dattawa a bangaren majalisa, yana mai cewa tsarin lissafin zai samar da daidaito ga ‘yan Najeriya.

Da yake mayar da martani dan majalisar dattijai, Sanata Abdulazeez Yari Abubakar, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya alkawuran da ya dauka na tabbatar da hadin kan Najeriya wadda take da buri na zama hamshakiyar kasa.

Yari ya ci gaba da cewa, idan aka zabe shi manufarsa ita ce yin aiki kafada da kafada da bangaren zartaswa domin ci gaban ‘yan Najeriya don jam’iyyar APC mai mulki ta cimma manufofinta tare da isar da ayyukan ta ga al’ummar Najeriya.

A cikin sakon nasa na fatan alheri tsohon ministan albarkatun man fetur, Umaru Dembo ya bukaci ‘yan siyasa da shugabanni da su kasance masu gaskiya a duka al’amuransu na yau da kullum.

Ya kara da cewa Najeriya za ta iya cimma burinta ne kawai idan mutane sun kasance masu gaskiya da rikin amana a duk wani mataki na ci gaban kasar.

Taron ya samu halartar Kungiyoyin tallafi daban-daban, masu fatan alheri da magoya bayan jam’iyyar All Progressive Congress APC.

Abdulkarim Rabiu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *