Take a fresh look at your lifestyle.

Neja Zata Samu Cigaba Karkashin Gwamna Umar Bago; Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazan Jihar.

Nura Muhammad

0 160

Shugaban hukumar jin dadin alhazan jahar Neja dake arewa ta tsakiyar Najeriya Alhaji Muhammad Awwal Aliyu ya yabawa gwamna Umar Mohammed Bago bisa tsare tsaren sa na ayyukan raya kasa da ya bayyana bayan karbar ragamar mulkin Jahar.

Mohammed Awwal Aliyu ya bayana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a garin Minna, inda ya ce batutuwan da mai girma Gwamnan ya gabatar a jawabin sa na farko bayan shan rantsuwa sune manyan matsalolin da Jahar Neja ke fuskanta a halin yanzun.

Shugaban hukumar ya Kara da cewar alummar jahar zasu ji dadin yadda mai girma Gwamna ya tsara kawo cigaba ta fannin ilimi da tsaro da Noma da kiwo da Kuma yadda zai taimakawa mata da matasa wajan ayyukan yi da bunkasa bangaran yawon bude Ido don farfado da mahimman kayayyakin tarihin da Jahar ke da su.

” Abu mafi mahimmanci shine yadda zai habaka ilimi da Samar da cigaba ga alummar jahar hakan zai bunkasa tattalin arzikin Jahar”. A cewar sa.

Da zarar ya kama aiki gadan gadan lalle za’a sami cigaba ta fannin ilimi da tsaro da Noma a dukkanin fading jahar.”

A karshe shugaban hukumar ya bayyana kudirin hukumar na baiwa mai girma gwamna Umar Mohammed Bago cikakken hadin Kai don ganin an sami nasara gudanar da aikin hajjin bana a kasa mai tsarki.

Alhaji Mohammed Awwal Aliyu ya ce babban burin hukumar shine na ganin ta kare martaba da kimar jahar Neja a gida da ma kasar Saudiya.

A Yan kwanakin nan dai hukumar jin dadin alhazan jahar Neja ta ta himmatu wajan ganin ta kammala dukkanin shirye shiryenta inda a makon da ya gabata ta fara rarrabawa alhazai kayayyaki.

Inda ko a wata sanarwar da Mai magana da yawun hukumar Danladi Hassan Idiris ya fitar ya nuna cewar shugaban hukumar na aiki tukuru don ganin alhazan jahar sun tashi daga filin jiragen sama kasa da kasa dake Minna fadar gwamnatin jahar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *