Take a fresh look at your lifestyle.

Ukraine Zata Kafa Wurin Sarrafa Makama

0 127

Ukraine ta ce tana aiki tare da babban kamfanin tsaro na Birtaniya BAE Systems don kafa wani sansani na Ukraine don samar da kuma gyara makamai daga tankunan yaki zuwa manyan bindigogi.

 

Shugaba Volodymyr Zelenskiy ne ya bayyana hakan bayan tattaunawa da manyan jami’ai na BAE da suka hada da shugaban gudanarwa Charles Woodburn.

 

Zelenskiy ya ce a cikin wani jawabi na faifan bidiyo na maraice, “Hakika babban mai kera makami ne, irin makamin da muke bukata yanzu kuma za mu ci gaba da bukata.”

 

Karanta kuma: Ukraine ta ba da sanarwar tura diflomasiyya ga Afirka

 

“Muna aiki don kafa tushe mai dacewa a Ukraine don samarwa da gyarawa. Wannan ya kunshi manyan makamai, tun daga tankokin yaki zuwa manyan bindigogi,” in ji shi. Zelenskiy bai bayar da ƙarin bayani ba.

 

Tun da farko, Zelenskiy ya ce bangarorin biyu sun amince su fara aikin bude ofishin BAE a Ukraine.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *