Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Kasa (INEC) Ta Bayyana Dan Takarar Jam’iyyar APC A Matsayin Wanda Ya Ci Zaben Kansilolin Kuje
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana dan takarar shugabancin jam’iyyar APC, Mista Danjuma Samuel Shekolo, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban karamar hukumar Kuje, a zaben babban birnin tarayya Abuja da aka kammala.
Babban jami’in da ke kula da zaben, Farfesa Nkiruka Odoh na Jami’ar Abuja, Najeriya, wanda ya bayyana sakamakon zaben da aka gudanar a ranar Asabar 21 ga watan Fabrairun 2026, ya ce Mista Shekolo ya samu kuri’u 17,269 inda ya doke abokin takararsa na jam’iyyar PDP, Mista Danlami Zakoyi, wanda ya samu kuri’u 15.8.
Da yake mayar da martani jim kadan bayan bayyana sakamakon zaben, Mista Danjuma Samuel Shekolo ya yabawa INEC kan yadda ta gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci.
Mista Shekolo ya kuma yabawa magoya bayansa da suka ba shi nasara a zaben.
Sai dai ya yi alkawarin isar da ribar dimokuradiyya ga al’ummar yankin Kuje
Aisha. Yahaya, Lagos