Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Tinubu Ya Karbi Bakuncin Gwamnonin Domin Buda Bakin Addinin Musulunci Na Ramadan

11

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya karbi bakuncin gwamnonin jihohin kasar nan, a wani taron buda baki na watan Ramadan a fadar gwamnati da ke Abuja, a ci gaba da al’adar sa na buda baki da shugabannin siyasa a cikin watan mai alfarma.

Bude azumin da aka fara da misalin karfe 7:00 na rana, ya kasance shekara ta uku a jere da shugaban kasar ya kira gwamnonin don gudanar da buda baki a fadar Aso Rock Villa.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, sun hadu da shugaban kasa a wajen buda baki, tare da mambobin majalisar zartarwa ta tarayya da kuma babban sufeton ‘yan sanda, Kayode Egbetokun.

Gwamnan jihar Imo kuma shugaban kungiyar gwamnonin Progressives’ Forum, Hope Uzodinma, ya jagoranci gwamnonin tarayya, ciki har da gwamnan jihar Abia, Alex Otti; Gwamnan jihar Cross River, Bassey Otu; Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf; Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia; da Gwamnan Jihar Ebonyi, Francis Nwifuru.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi; Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani; Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu; Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang; Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori; Gwamnan jihar Ekiti, Biodun Abayomi Oyebanji; da gwamnan jihar Edo, Monday Okpebolo.Mataimakin gwamnan jihar Bauchi ma ya halarta.

A bukin buda baki da ya gabata, shugaba Tinubu ya yi amfani da wannan dama wajen inganta hadin kan kasa da karfafa hadin gwiwa a tsakanin jam’iyyar.

Ana sa ran karin tarukan buda baki a fadar gwamnati a cikin kwanaki masu zuwa yayin da ake ci gaba da gudanar da bukukuwan Azumin watan Ramadan

 

Aisha. Yahaya, Lagos

Comments are closed.