Kasashen Sin da Najeriya sun jaddada karfafa gwiwar mata a matsayin mabudin ci gaban kasa tare da jaddada aniyarsu na hadin gwiwa wajen daidaita jinsi, ilimi da mu’amala tsakanin jama’a.
An bayyana hakan ne a Abuja, a wajen bikin sabuwar shekara ta kasar Sin, bikin fitulu da bikin murnar matan Sin da Najeriya.
Da yake jawabi a wurin taron, darektan cibiyar al’adun kasar Sin, Mista Yang Jianxing, ya ce bikin ya nuna dabi’u iri daya, da kara dankon zumunci a tsakanin kasashen biyu.
Mista Jianxing ya jaddada cewa, miliyoyin mata a kasashen Sin da Najeriya suna ba da gudummawa sosai ga iyalansu, da wuraren aiki, da kuma ci gaban kasa.

Mista Jianxing ya ce; “Wannan ra’ayi ya zama tushen al’adu mai zurfi na falsafar “al’umma mai kyakkyawar makoma ga bil’adama” na kasar Sin, a sa’i daya kuma, muna son yin amfani da bikin na yau don nuna farin ciki da kuma yaba wa gagarumar gudunmawar da mata suka bayar wajen ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’umma, da kuma tabbatar da muhimmin ra’ayi kan cewa, ta hanyar tabbatar da mata sun samu damar samun ilimi da guraben aikin yi, za su iya samun ci gaba mai girma a duniya.
A cewarsa, kasar Sin ta aiwatar da sanarwar birnin Beijing, da kare hakkin mata da kuma samun gagarumin ci gaba.
Mista Jianxing ya bayyana cewa, mata miliyan 690 a kasar Sin sun samu daidaiton al’umma mai matsakaicin wadata, inda mata ke da sama da kashi 40% na ma’aikata, sama da rabin masu sana’ar intanet.
Shi ma da yake jawabi, shugaban ofishin UNESCO na Abuja, Jean-Paul Ngome Abiaga, ya bayyana bikin a matsayin ‘shaida ga al’adu da gina gadoji tsakanin Najeriya da kasar Sin.
Ya yi kira da a yi hadin gwiwa da aiki tare, yana mai bayyana irin matakan da kasar Sin ta dauka wajen inganta daidaiton jinsi.
Babban Sakatare na dindindin na ma’aikatar fasaha, al’adu, yawon bude ido da tattalin arzikin kasa ta Najeriya, Mukhtar YawaIe Muhammad ya ce bikin ya nuna hadewar manyan wayewa guda biyu, tare da mata a matsayin manyan masu kula da al’adu da kirkire-kirkire.

Taron ya tattaro manyan jami’an gwamnati, jami’an diflomasiyya, da abokan ci gaba, tare da hada shagulgulan al’adu tare da sabunta alkawuran fadada damammaki ga mata.
A’isha. Yahaya, Lagos