Take a fresh look at your lifestyle.

GWANATIN JIHAR BARNO TA TALLAFAWA ‘YAN GUDUN HIJIRA SANADIYAR AMBALIYAR RUWA

0 231

Ruwan sama kamar da bakin kwarya a jihar Barno dake Arewa maso gabashin Najeriya ya haifar da ambaliyar Ruwa a Karamar Hukumar Damboa mai tazarar tazarar Kilo mita 85 daga garin Maiduguri Babban Birnin jihar Barno, wanda ya yi sanadiyyar asarar Dukiyoyi, Gidaje da Gonaki.

 

Gwamnan jihar Barno Furofesa Babagana Umara Zulum, ya kai ziyarar gani da ido don jajantawa al’umar yankin da abin ya shafa tare da basu gudunmuwar Kudi Naira Miliyan Dari 172, da Kayayyakin Abinci.

 

A kalla Mutane Dari 436 akayi kiyasin cewar wannan Ambaliyan Ruwan

Saman  da aka tafka kamar da bakin Kwarya har na tsawon kwanaki biyu

babu kakkautawa,wanda ya sanya al’umar yankin yin hijira zuwa wasu yankuna domin samun mafaka ,daga cikin wadanda abun ya shafa har da Kananan Yara da Mata.

 

Sama da Mutane Dubu 30 ne, suka Amfana dagaTallafin da Gwamnan Jihar Borno da kuma samar masu da isasshen Abinci, Tufafin Sawa da hanyoyin gudanar da aikin Noma cikin sauki.

 

A karshen ziyarar gwamnan, ya duba yanayin sabon ginin Makarantar

Sakandare na Zamani, da za’a rika koyar da Ilimin Addini da na

Zamani, kamar yadda ya bayar da umarnin gina irin wadannan Makarant a

ko wane Yankin Karamar Hukuma 27 dake fadin jihar, da nufin bunksa

ilimin Addini da na Zamani.

 

Tijjani Usman Bello

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *