Rundunar hadin gwiwa ta Multinational Joint Task Force, MNJTF ta ce ta kuduri aniyar cewa ba za ta bar duk wani tsibiri na tafkin Chadi domin ‘yan ta’adda su kai farmaki ba.
Kwamandan rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa (MNJTF), Manjo Janar Gold Chibuisi ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar aiki da ya kai Blangoua a Kamaru, Bagasola da Bibi a Jamhuriyar Chadi a karkashin sashe na 1 da na 2.
Wata sanarwa da babban jami’in yada labarai na rundunar sojin MNJTF N’Djamena na kasar Chadi Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi ya fitar ta ce, Manjo Janar Chibuisi ya jaddada cewa manufar ziyarar ita ce tantance irin karfin da kungiyar ta MNJTF ke da shi.
Ya bukaci sojojin da su ci gaba da jajircewa wajen bayar da goyon bayansu ga aikin karfafa nasarorin baya-bayan nan da aka samu a lokacin Operation Lake Sanity.
Tun lokacin da aka fara aikin, Operation Lake Sanity ya raunana karfin ’yan Boko Haram wajen tsarawa da gudanar da ayyukansu a tsibiran tafkin Chadi da aka fi sani da “Tumbus”.
Ziyarar gudanar da aiki a kasashen Kamaru da Chadi na zuwa ne kwana guda bayan ziyarar makamanciyarta da suka kai Malam-Fatori a Najeriya da Diffa da kuma Bosso na Jamhuriyar Nijar wanda ke ci gaba da kokarin murkushe ta’addanci da tada kayar baya a yankin tafkin Chadi.
Kungiyar MNJTF ta taka rawar gani wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Ziyarar Kwamandan Rundunar na da niyyar karfafa kwarin gwiwar sojojin da kuma nuna goyon bayansa ga ayyukan da ake gudanarwa.
Ziyarar ta kuma kara karfafa kudurin MNJTF na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin da kuma dawo da kwarin gwiwar al’ummar yankin.
Leave a Reply