Take a fresh look at your lifestyle.

Jami’an Tsaron Somaliya Sun Kawo Karshen Kashe Kashe Da ‘Yan Ta’adda Ke Yi A Wani Otal

0 167

Kafofin yada labaran kasar Somaliya sun rawaito cewa, jami’an tsaron kasar sun kawo karshen kawanyar da aka yi wa wani otel a Mogadishu babban birnin kasar.

Rundunar ‘yan sandan ta ce an kashe fararen hula 6 tare da jikkata wasu 10.

Mayakan kungiyar ‘yan ta’adda sun dauki alhakin harin da aka kai a ranar Juma’a 9 ga watan Yuni a kudancin babban birnin kasar.

Shaidu sun ba da rahoton jin karar harbe-harbe da fashe-fashe.

“A daren yau, mun ga wani babban bala’i a bakin tekun Liido da ke gundumar Abdiaziz a lokacin da nake jin dadi da abokina,” in ji Yahye Mohamed wanda ya shaida lamarin.

“Da tashin bom na farko, na ga wata mata ta fado kasa, ta mutu, bayan da fashewar ta same ta. Allah ya jikan wadanda aka kashe.”

Kungiyar Al-Qaida ta Gabashin Afirka, al-Shabab, ta shahara wajen kai hare-hare a otal-otal da sauran manyan wurare a Mogadishu, yawanci farawa da harin kunar bakin wake.

Otal din Pearl Beach yana kan titi daga ofishin jakadancin Turkiyya kuma ya shahara da jami’an gwamnati.

Hassan Abdirahman ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Associated Press cewa yana cikin gidan abincin a lokacin.

“Na ji karar harbe-harben bindiga wanda ya fito daga bakin gabar teku sannan da karar fashewar wani abu.” Ya ce ya tsere ya ga barnata motoci a bakin titi.

Mulki Osman ya kuma ce shi da abokansa “nan take suka gudu domin boye” a cikin gidan abincin lokacin da suka ji karar fashewar wasu abubuwa da harbe-harbe jim kadan kafin karfe 8 na dare.

“Wasu abokaina har yanzu suna makale a cikin otal din, amma jami’an tsaro sun yi nasarar kubutar da ni. Ina fatan sun zauna lafiya,” inji shi.

Tekun Liido yana daya daga cikin fitattun wurare a Mogadishu kuma yana cike da aiki a daren Juma’a yayin da ‘yan Somaliya ke jin daɗin karshen mako ta ziyartar shagunan kofi na gida da wuraren shakatawa na ice cream.

A shekarar da ta gabata, shugaban kasar Somaliya, Hassan Sheikh Mohamud, ya kaddamar da “yaki na bai-daya” kan ‘yan ta’adda, tare da hada kan Somaliyan da su taimaka wajen fatattakar ‘yan kungiyar da ya bayyana a matsayin “kwari”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *