Tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom da ke Kudancin Najeriya, Sanata Godswill Akpabio ya zama shugaban majalisar dattawan Najeriya ta 10, bayan zabensa da aka yi ranar Talata.
Shi ma Sanata Jibrin Barau ya zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ba tare da hamayya ba, tare da goyon bayan dukkan Sanatoci 109. Ya fito daga jihar Kano, Arewacin Najeriya.
Zaben nasu shi ne manyan abubuwan da suka faru a ranar Talatar da ta gabata na kaddamar da majalisar dattawa ta 10, biyo bayan ayyana majalisa ta 10 da shugaba Bola Tinubu ya yi.
Zaben da aka yi ta kaure ya nuna Sanata Godswill Akpabio ya doke abokin takararsa Sanata Abdulaziz Yari, wanda kuma tsohon gwamnan jihar Zamfara ne da ke arewacin Najeriya.
Sanata Akpabio ya samu kuri’u sittin da uku (63) inda ya doke Sanata Yari wanda ya samu kuri’u 46.
Fita Daga Takara
Sakamakon zaben kamar yadda magatakarda na majalisar, Mista Sani Tanbawal ya sanar, tun da farko ’yan takara biyu, Sanata Orji Uzor Kalu da Osita Izunaso sun fice daga takarar kafin zaben.
An fara zaben Sanata Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattijai ne da Sanata Mohammed Ali Ndume ya nada shi, kuma Sanata Solomon Olamilekan ya goyi bayan nadin.
Hakazalika, tsohon gwamnan jihar Ebonyi, Sanata David Umeahi ya zabi Sanata Jibrin Barau a zaben sa, kuma Sanata Salihu Mustapha ne ya mara masa baya.
Yawancin Sanatocin da suka zanta da Muryar Najeriya da suka hada da Sanata Victor Umeh da Neda Imasuen ‘yan jam’iyyar Labour, sun yi imanin cewa dole ne majalisar dattawa ta ba da fifiko kan harkokin tsaro da farfado da tattalin arzikin kasar domin dawo da Najeriya kan turbar ci gaba.
Achat en ligne de médicaments sans prescription médicale Ebewe Los Andes médicaments pas cher
Belgique
où acheter du médicaments sans ordonnance Ranbaxy Poperinge Acheter médicaments
en toute sécurité
contact алматы, contact астана переломы таза
классификация, перелом вуальмье слушать кисло-сладкий, кисло-сладкий все песни скачать таптым ау сені remix, таптым ау сені
текст