Mataimakin Shugaban Najeriya, Sanata Kashim Shettima da Shugaban Gidauniyar Bill and Melinda Gates, Bill Gates, da Shugaban Gidauniyar Dangote na ganawa da kungiyar gwamnonin Najeriya a halin yanzu.
Taron wanda aka fara shi da misalin karfe 11:45 na safe agogon Najeriya, yana gudana ne a dakin taro na fadar gwamnati dake fadar shugaban kasa a Villa Abuja.
A ranar Litinin din da ta gabata ne Gates ya gana da shugaban kasa Bola Tinubu a wani bangare na shirin domin koyo daga abokan hulda da ke taimakawa wajen magance cutar shan inna, karancin jini, da sauran matsalolin kiwon lafiya.
A wani taro makamancin haka a shekarar 2018, Gates ya ce shirin farfado da tattalin arzikin Najeriya, (ERGP), na bukatar ya kara zama a kan yadda kasar za ta magance matsalolin lafiya da ilimi.
Leave a Reply