Take a fresh look at your lifestyle.

Hukuma Zata Daukaka Kara Kan Tsohon Shugaban JAMB

0 124

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya, da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da sauran Laifuka Masu Zaman Kanta (ICPC) ta ce za ta daukaka kara kan hukuncin da wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke kan karar da tsohon Shugaban Hukumar, Dibu Ojerinde Ya shigar tare da kararraki ta kasa da kasa. 

Kotun dai ta ci tarar hukumar diyyar naira miliyan daya da kuma naira dubu 200,000, bisa kamawa da tsare Farfesa Dibu Ojerinde bisa zargin aikata almundahana.

Sanarwar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta fitar ta hannun kakakinta Mrs Azuka Ogugua ta ce tana da sahihin sammacin da babban alkalin babbar kotun tarayya ya bayar a ranar 6 ga watan Disamba 2022.

Professor Ojerinde ya yi amfani da sunaye da dama na karya, laqabi da kuma hanyoyin tantancewa na jabu irin su Akanbi Lamidi, Adeniyi Banji, Habibulahi Lamidi, Joshua Olaniran Olakuleyin, da dai sauransu wajen cin hanci da rashawa ta hanyar asusun banki daban-daban kuma har yanzu yana rike da dukiya da tasiri don gujewa shari’a.”

Ogugua ya lura cewa hukumar ta ci gaba da kasancewa cikin damuwa kuma za ta ci gaba da sauke nauyin da ke kanta tare da himma da kwarewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *