Take a fresh look at your lifestyle.

Majalisar Wakilai Na Ci Gaba Da Tantance Manyan Hafsoshi

0 166

A halin yanzu dai ana ci gaba da tantance manyan Hafsoshi da majalisar wakilai ta nada a harabar majalisar dokokin tarayya Abuja.

 

 

 

Wani kwamitin wucin gadi da kakakin majalisar wakilai Tajuddeen Abbas ya kafa ne ke gudanar da tantancewar wanda wani bangare ne na ka’idojin tabbatar da karshe na hafsoshin tsaron kasar.

 

 

Shugabancin majalisar ne ke gudanar da tantancewar, sannan kwamitin wucin gadi na majalisar kan tantance manyan Hafsoshin tsaro na karkashin jagorancin Hon Babajimi Benson, tare da dukkanin manyan jami’an majalisar guda takwas da suka fito daga jam’iyyu masu rinjaye da marasa rinjaye a matsayin mambobi.

 

 

Wadanda aka nada sun hada da babban hafsan tsaro Manjo Janar Christopher Musa, shugaban hafsan soji, Manjo Janar Abiodun Lagbaja, babban hafsan sojin ruwa Rear Admiral Emmanuel Ogalla, da babban hafsan sojin sama, Vice Marshal Hassan Abubakar.

 

L.N

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *