Dangane da yadda jami’an tsaro ke yawan lalata jiragen ruwa makil da danyen mai, Majalisar Wakilan Najeriya ta bukaci hukumomin tsaro na gwamnatin tarayya da su kau da kai daga irin wadannan ayyuka.
Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin da dan majalisa daga jihar Delta Mista Thomas Ereyitomi ya gabatar a zauren majalisar.
Dan majalisar ya ce hakan na da nufin dakile gurbacewar muhalli a yankin Neja Delta.
Mista Ereyitomi ya lura cewa kona jiragen ruwa da aka sata dauke da danyen mai zai kara ruguza muhallin yankin Neja-Delta da ya riga ya lalace sakamakon hakar mai.
“Majalisar ta lura da rahotannin da aka samu kwanan nan na kutsawa, kamawa da lalata wasu jiragen ruwa makare da danyen mai a yankin Neja Delta, na baya-bayan nan shi ne MT TURA II a ranar Juma’a 7 ga Yuli, 2023 a cikin kogin escravos a karamar hukumar Warri ta Kudu-maso-Yamma. Area, Jihar Delta.
“Har ila yau, ya lura cewa jirgin MT TURA, mai karfin tan 800,000 ne a lokacin da aka kama shi da kuma lalata shi, dauke da kimanin tan 150,000 na danyen mai na sata. An kuma kara da cewa, tawagar hadin guiwar jami’an tsaron Najeriya da wakilan NNPC Ltd. sun kona jirgin a ranar 11 ga watan Yuli, 2023.
“Sanin cewa a watan Oktoban 2022, an kama wani jirgin ruwa mai suna MTDEIMA wanda ke dauke da tan 1500 na danyen mai na sata, an kuma kona shi a kogin Warri escravos.”
Da yake amincewa da kudirin, ya kuduri aniyar kafa kwamitin da zai binciki dalilan da suka sa jami’an tsaro suka lalata jiragen ruwan da ke dauke da mai.
Majalisar ta kuma umarci kwamitocin muhalli da sauyin yanayi (lokacin da aka kafa) su tabbatar da bin ka’ida.
Leave a Reply