Gwamnatin jihar Ebonyi ta ce za ta raba buhunan takin zamani 13,000 ga manoma, a wani mataki na bunkasa noman abinci.
Mista Chikadibia Okpor, kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a na jihar ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai bayan taron kolin mako na jihar a Abakaliki.
A cewarsa, Gwamnan Jihar Mista Francis Nwifuru, a yayin taron Majalisar Zartaswar Jihar, ya samu rahoton fara samar da taki da Kamfanin Taki da Sinadarai na Jihar.
Ya ce rahoton ya yi daidai da umarnin taron majalisar da ya gabata.
“Saboda haka jihar ta amince da sayo tare da raba buhunan takin zamani 13,000 ga manoma.
Okpor ya ce, “A kan gyaran raka’a 33 na taransfoma domin sake tura wutar lantarki a fadin jihar, majalisar ta yanke shawarar umurci kwamishinan wuta da makamashi da ya tuntubi kamfanin rarraba wutar lantarki na Enugu (EEDC),” inji Okpor.
L.N
Leave a Reply