Uwargidan shugaban Najeriya, Oluremi Tinubu a ranar Alhamis ta kai ziyarar ban girma ga tsohon shugaban kasar, Mohammadu Buhari a gidansa da ke Daura, jihar Katsina.
Misis Tinubu, wacce ta samu rakiyar uwargidan mataimakin shugaban kasa, Nana Shettima, ta ce sun kai ziyarar ne domin duba tsohon shugaban kasar tare da gode masa bisa goyon bayan uba da yake ci gaba da baiwa gwamnatin mai ci.
Ta kuma yi addu’ar Allah ya ba shi lafiya, ya kuma kara masa goyon baya ba kawai ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba har ma da Nijeriya baki daya.
A nasa jawabin tsohon shugaban, wanda ya nuna jin dadinsa, ya bayyana cewa ziyarar ta yi matukar ban mamaki.
“Kamar yadda kuke gani, ta zo ta duba ni ta ga cewa ina lafiya,” in ji shi.
PIAK
Leave a Reply