Take a fresh look at your lifestyle.

KWAMISHINONI TARA MAJALISAR DOKOKIN JIHAR KANO TA ZABA

0 126

A ranar Litinin majalisar dokokin jihar Kano ta amince da nadin kwamishinoni Tara da Gwamnan jihar Abdullahi Ganduje,ya mika mata.

A taron ta ranar Litinin, Mai gabatarwa Hon Hamisu Ibrahim-Chidari, yace Majalisa ta sanar da Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa ya kasance a jerin Zababbu.

Kamar yadda  kakakin majalisa y asana, an aike da  takardar gayyatar Dr. Aminu Ibrahim-Tsanyawa ya gabatar da kanshi ga auren taron majalisa ranar Talata<domin tantance shi.

Sababbin Kwamishinonin sun hada da: Ibrahim Dan’azumi, Abdulhalim Abdullahi, Lamin Sani-Zawiyya,Ya’u Abdullahi-Yan’shana, Garba Yusuf Abubakar da Dr. Yusuf Jibirin.

Sauran sune Adamu Fanda, Saleh Kausami, da Dr. Ali Burum Burum.

A madadin ‘yan uwan shi, Dr. Ali Burum-Burumya yaba wa yadda Majalisar ta gudanar da tantancewar.

“Zan yi kokari na domin ganin na goya wa Gwamna, Dr. Abdullahi Ganduje, baya wajen cimma burin kawo ci gaban kano,”  Inji Dr. Burum-Burum.

 

LADAN NASIDI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *