Take a fresh look at your lifestyle.

VP Shettima Manyan Baki Suka Halarci Daurin Auren Dan Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa

85

A ranar Juma’a da ta gabata Tsohon birnin kasuwancin Kano ya samu halartar manyan baki, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, mai rike da tutar jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas suka halarci daurin auren Abdullahi Dan mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin.

 

 

An gudanar da daurin auren a masallacin Juma’a na Isyaku Rabi’u, mataimakin shugaban kasa a matsayin wakilin angon yayin da kakakin majalisar wakilai Rt. Tajudeen Abbas ya tsaya wa amaryar, Bilkisu Madaki, diyar mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai, Sanata Aliyu Sani Madaki.

 

 

Babban Limamin Masallacin, Sheikh Abdullahi Mahmud Salga ya daura aure tsakanin Abdullahi da Bilkisu bayan an biya sadakin amarya N500,000.

 

Daurin auren ya samu halartar manyan baki da suka hada da gwamnoni, ‘yan majalisa, ‘yan siyasa, da sauran masu hannu da shuni.

 

 

 

A halin da ake ciki, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana kasancewar Peter Obi a wurin daurin auren a matsayin alamun dunkulewar Nijeriya.

 

Akpabio a lokacin da yake jawabi jim kadan bayan daurin auren ya bayyana cewa halartar manyan mutane da dama a wajen daurin auren Fatiha sun tabbatar da cewa Sanata Barau Jibrin mutum ne mai zaman lafiya.

 

 

“Kuna iya ganin hatta dan takarar shugaban kasa na LP Peter Obi da jama’arsa suna nan, wannan ya nuna muku cewa Najeriya za ta ci gaba da kasancewa a dunkule a matsayin kasa daya”.

 

 

Shugaban Majalisar Dattawa, ya shawarci Dan da Diyar Barau Jibrin da Ali Madaki da suka aura da su tashi cikin kwanciyar hankali da soyayya da kuma hakuri da juna.

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.