Take a fresh look at your lifestyle.

Zaftarewar kasa a Habasha ta kashe mutane 52 da dama sun bata

135

Akalla mutane 52 ne aka tabbatar sun mutu sakamakon zaftarewar kasa a shiyyar Gamo da ke kasar Habasha a farkon makon nan.

 

Hukumomin kasar sun ce wasu kimanin 50 ne har yanzu ba a gansu ba bayan zaftarewar kasa da ta afku sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a yankin.

 

A cikin wata sanarwa da ofishin yada labarai na shiyyar Gamo ya fitar ya ce kungiyoyin ceto na ci gaba da gudanar da bincike.

 

KU KARANTA KUMA: Zabtarewar kasa ta DRC ta yi ikirarin rayuka sama da 200

“An tabbatar da cewa mutane 52 ne suka rasa rayukansu kuma ana ci gaba da kokarin gano mutane 50 da ba a san inda suke ba” in ji ofishin.

 

Jami’ai daga gwamnatin yankin a Habasha ma sun tabbatar da adadin wadanda suka mutu.

A cewar kafar yada labarai ta kasar Habasha mazauna yankin sun taru a wurin da bala’in ya afku inda aka kori ciyayi a sassan wani tudu.

 

An ga wasu mutane sun durkusa cikin laka yayin da ake ci gaba da aikin ceto.

 

Rahotanni sun bayyana cewa zaftarewar kasa ba sabon abu ba ne a sassan kudancin kasar Habasha a lokacin damina yayin da mamakon ruwan sama na iya raunana tudun mun tsira tare da janyo rugujewar kasa kwatsam.

 

Comments are closed.