Take a fresh look at your lifestyle.

Najeriya Ta Karfafa Dangantaka Da Switzerland

141

Najeriya da Switzerland sun amince da karfafa dangantakarsu ta biyu tare da mai da hankali kan tsarin da ya kunshi fannoni da dama da suka hada da kasuwanci hadin gwiwar tattalin arziki da samun kwarewar aiki da hijira da tsaro da musayar al’adu.

 

Mataimakin shugaban Najeriya ya karbi takwaransa na Switzerland da matarsa Paola Cassis a ranar Talata a reshen shugaban kasa na Nnamdi Azikiwe International Airport Abuja inda suka hadu a bayan kofofin da aka rufe.

 

Da yake jawabi ga ‘yan jarida bayan taron Mataimakin Shugaban Kasa Cassis wanda kuma shi ne Ministan Harkokin Wajen Switzerland ya bayyana cewa tattaunawar ta mayar da hankali ne kan inganta dangantakar kasashen biyu da yarjejeniyar cinikayya ta kyauta da samun kwarewar aiki da ƙaura  musayar al’adu da tallafawa Najeriya wajen magance matsalar tsaro a yankin Arewa maso Gabas.

 

KU KARANTA KUMA: Kasar Sin Ta Sake Jaddada Jajircewar Karfafaa Dangantakar Kasashen Biyu Da Najeriya.

Ya ce: “Muna la’akari da inganta dangantakarmu ta biyu. Muna tunanin nazarin damar yin yarjejeniyar cinikayya tare da dangin AfCFTA da Najeriya. Abu na biyu, muna aiki tare sosai a kokarin diflomasiyya don magance rikice-rikice daban-daban a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

 

” Na uku muna ba da gudummawa ga horar da sana’a a Najeriya tare da kamfanonin Switzerland a Najeriya suna samar da mafi kyawun yanayi ga matasa su zauna tare cikin lumana ta hanyar samun ƙwarewar da za su sami aikin yi a nan gaba.”

Kayayyakin Tarihi

 

Ministan ya bayyana cewa gwamnatin Switzerland ta kuma amince ta mayar da tagulla da kayan tarihi na masarautar Benin a jihar Edo a matsayin wani bangare na kokarin karfafa alakar al’adu tsakanin kasashen biyu.

Comments are closed.