Gwamnan jihar Binuwai, Hyacinth Alia, ya roki hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta JAMB da ta sake tsara jarabawar dalibai takwas daga jihar da aka sace a lokacin da suke tafiya domin zana jarabawarsu ta bai daya.
Gwamnan ya yi wannan roko ne a gidan gwamnati da ke Makurdi a daidai lokacin da kwamishinan ‘yan sandan jihar Binuwai, Ifeanyi Enemari, ya gabatar da wadanda aka ceto guda 18 a gabansa.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar za ta bai wa daliban da abin ya shafa tallafin karatu don tallafa musu.

Gwamna Alia ya umurci Kwamishinan Lafiya da Ayyukan Jama’a da ya tabbatar da cewa wadanda abin ya shafa sun samu tantance lafiyarsu kyauta a asibitin koyarwa na jami’ar jihar Benue.
KU KARANTA KUMA: Hukumar JAMB za ta sake tsara jarabawar UTME ga wadanda abin ya shafa
Da yake jaddada kudirin gwamnatinsa na magance matsalar rashin tsaro, gwamnan ya yabawa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro bisa kokarin da suke yi na ceto wadanda lamarin ya shafa da kuma ci gaba da matsin lamba ga masu aikata laifuka.

Ya bayyana cewa an kama mutane bakwai da ake zargin ‘yan kungiyar masu garkuwa da mutane ne, sannan ya bukaci hukumomin tsaro da su kara kaimi don kare mazauna yankin.
Gwamna Alia ya kuma yabawa Sufeto Janar na ‘yan sanda bisa yadda ya tura tawagar kwararru da suka taimaka wajen samun nasarar aikin ceto.
A’isha. Yahaya, Lagos