Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Adamawa, ADSEMA, ta tabbatar da cewa ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutane akalla biyar a sassa daban-daban na jihar Adamawa arewa maso gabashin Najeriya.
Sakataren zartarwa na ADSEMA, Dr Suleiman Muhammad ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, a Yola ranar Alhamis.
Muhammad ya kara da cewa gidaje da wuraren kasuwanci da dama kuma ambaliyar ta shafa a kananan hukumomin Fufore, Yola ta Kudu, da Mubi ta Kudu.
Don haka sakataren zartaswar ya shawarci mazauna yankunan kogunan jihar da su kara yin taka tsantsan sakamakon rufe madatsar ruwa ta Lagdo a Kamaru.
Ya ce a kwanakin baya hukumar ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki inda ta bukaci mazauna al’ummomin da ke fama da ambaliyar ruwa da su koma wuraren da suka fi tsaro.
Muhammad ya ce har yanzu ana ci gaba da gudanar da gangamin wayar da kan jama’a game da ambaliyar ruwa a fadin kananan hukumomi 21 na jihar.
“An shawarci mazauna yankunan da ke fama da ambaliyar ruwa da su bi umarnin da kwararru suka bayar. Dole ne su yi taka tsantsan.
“Karin ruwan sama zai sauka, ba za mu iya cewa ya kare ba tukuna. Dole ne mutane su kasance masu lura da tsaro,” in ji shi.
Shugaban ADSEMA ya bayyana kudurin hukumar na gudanar da aikinta yadda ya kamata na tafiyar da al’amuran gaggawa a jihar.
NAN/Ladan Nasidi
Leave a Reply