Take a fresh look at your lifestyle.

Taron G-20: Shugaba Tinubu Ya Gana Da Shugabannin Tsaro

0 198

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gana a takaice da manyan hafsoshin tsaron shi domin karbar bayanai daga gare su sakamakon gudanar da ayyukansu gabanin tafiyar da suka yi a Indiya domin halartar taron G-20.

Taron wanda aka saba gudanarwa a fadar shugaban kasa ta Villa, ya samu halartar babban hafsan tsaron kasa, Janar Christopher Musa, babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, da takwaransa na sojojin ruwa, Admiral Emmanuel Ogalla da kuma babban hafsan sojin sama, Air. Marshal Hassan Abubakar.

Taron wanda ya gudana a bayan fage, a fadar shugaban kasa, ya yi wa shugaban kasar karin bayani kan yanayin tsaro a kasar nan, ciki har da nazarin wuraren da shugabannin ma’aikata ke bukatar ingantawa kan kokarin dinke baraka.

Daga baya kuma a ranar Litinin ne shugaba Tinubu ya fara tafiyarsa zuwa birnin New Delhi na kasar Indiya domin halartar taron shugabannin kasashen G-20 da aka shirya gudanarwa tsakanin ranakun 9 zuwa 10 ga watan Satumba.

 

Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *