Take a fresh look at your lifestyle.

Ministan Yada Labarai Ya Taya Etsu Nupe Murnar Cika Shekaru 71 Da Haihuwa

0 97

Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Najeriya, Mohammed Idris, ya aike da sakon taya murna ga mai martaba Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar, shugaban majalisar sarakunan jihar Neja, bisa cikarsa shekaru 71 da haihuwa da kuma bikin cikar Shekara 20 da hawan karagar mulki.

Etsu Nupe ya kasance shugaban da ya cancanta wanda ya nuna hikima ta musamman ga al’ummarsa, wanda kuma gwamnatocin jihar Neja da na tarayya suka amfana a cikin shekaru ashirin da suka gabata,” in ji Ministan a cikin wata sanarwa.

Babu shakka cewa mulkinsa ya shaida zaman lafiya da wadata a Nupeland kuma zai ci gaba da zama albarka ga mutanensa da al’ummarsa.”

Kabilar Bida, ƙabila ce ƴan asalin Arewa ta Tsakiyar Najeriya, sune manyan ƙabilu a jihar Neja. Haka kuma suna nan a jihar Kwara, jihar Kogi da kuma babban birnin tarayya.

Ministan wanda ke rike da kambun Kakaki Nupe (Mai magana da yawun al’ummar Nupe) ya yi bikin ne domin taya al’ummar Nupe murna bisa gagaruman nasarorin da mai martaba ya samu, wanda a cewarsa, ya kasance abin koyi a tsakanin sarakunan Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *