Har yanzu dai halin da ake ciki a unguwar Seme-Krake na babban birnin kasar Benin na Cotonou na ci gaba da dauriya, yayin da iyalai ke alhinin ‘yan uwan su da suka mutu a wata gobara da ta tashi a wani wurin ajiyar man da aka haramta shigo da shi.
Har yanzu dai akwai jami’an tsaro sosai a yankin, wani mutum ya ce ya rasa ‘yan uwa hudu a gobarar.
“Ba mu san inda gobarar ta tashi ba kuma akwai mutane da yawa a cikin rumbun ajiyar. Ni kaina ina da mutane hudu daga cikin iyalina waɗanda suka mutu a cikin wuta. Kanena – uba daya, uwa daya da babban dansa, matar dan uwana da matar surukina,” in ji Antoine Djanta, wani mai shago.
Kasar Benin dai ita ce babbar hanyar safarar man fetur daga makwabciyar kasar Najeriya.
Hatsarin gobara a matatun mai da bututun mai da kuma rumbunan mai ya zama ruwan dare a Najeriya ma.
Da yawa daga cikin ‘yan kasar Benin ne ke rayuwa ta hanyar siyar da man da aka hana shigowa da su.
Shawarar da gwamnatin Najeriya ta yanke a watan Mayu na kawo karshen tallafin man fetur ya haifar da tashin gwauron zabi na farashin mai, wanda ya kara sha’awar fasakwaurin mai.
Africanews/ Ladan Nasidi.
Leave a Reply