A ranar litinin ne hukumar mulkin kasar Mali ta sanar da dage zaben shugaban kasar da aka shirya gudanarwa a watan Fabrairun shekarar 2023.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnati Abdoulaye Maïga ya shaidawa manema labarai a Bamako cewa za a dage ranar da aka fara gudanar da zabukan zagaye biyu na ranakun 4 da 18 ga watan Fabrairun 2024, saboda wasu dalilai na fasaha.
Daga cikin wadannan dalilai na fasaha, hukumomi sun ba da misali da abubuwan da ke da nasaba da amincewa da sabon kundin tsarin mulki a farkon wannan shekara da kuma sake fasalin kundin zabe.
Har ila yau, sun ba da misali da wata takaddama da wani kamfani na Faransa mai suna Idemia, wanda suka ce yana da hannu wajen aikin kidayar jama’a.
Gwamnati ta ce za a bayyana sabbin ranakun da za a gudanar da zaben a wani mataki na gaba.
Mali ta gudanar da kuri’ar raba gardama a watan Yuni, 2023, kan sabon kundin tsarin mulki wanda ya karfafa ikon shugaban kasa da kuma baiwa sojojin kasar alfahari.
Duk da sukar da aka yi wa daftarin tsarin mulkin, kuri’ar “e” ta yi nasara, inda aka kirga kashi 96.91 na kuri’un da ke goyon bayan tsare-tsaren.
Africanews/ Ladan Nasidi.
Leave a Reply