Take a fresh look at your lifestyle.

Daruruwan Almajirai Da Ambaliyar Ruwa A SA Aka Ceto

1 191

An ceto yaran makaranta da dama bayan ambaliyar ruwa da ya mamaye su a wani wurin shakatawa na tsawon kwanaki uku a Afirka ta Kudu.

 

 

Kungiyar wacce ta kunshi dalibai 72 da malamai 10 daga makarantar firamare ta Aliwal North, sun makale a gidan shakatawa na Cango Mountain da ke Oudtshoorn a ranar Lahadin da ta gabata, bayan da kogin da ya ratsa ta otal din ya cika.

 

 

Magajin garin Oudtshoorn Chris Macpherson ya shaidawa jaridar Times Live cewa daliban sun sami damar barin wurin shakatawa da safiyar Laraba.

 

 

“Kogin ya lafa da daddare ta yadda motoci za su iya tafiya a kan gadar ruwa mara kyau,” in ji Mista Macpherson.

 

 

A ranar Talata, wani jirgin sama mai saukar ungulu na gaggawa ya ba da abinci da ruwa ga kungiyar da ta makale.

 

 

An fara ruwan sama kamar da bakin kwarya a karshen mako kuma ya kai har yammacin Talata.

 

 

Koguna da dama a fadin lardin Western Cape sun yi ambaliya, wanda ya haifar da lalacewar ababen more rayuwa da kuma katsewar wutar lantarki.

 

 

A birnin Cape Town mutane takwas ne wutar lantarki ta kama a cikin mummunan yanayi, yayin da aka kwashe daruruwan wasu daga gidajensu.

 

 

BBC/ Ladan Nasidi.

One response to “Daruruwan Almajirai Da Ambaliyar Ruwa A SA Aka Ceto”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *