Take a fresh look at your lifestyle.

Sojojin Indiya Sun Bace A Ambaliyar Ruwa

0 81

Sojojin Indiya 23 ne aka bayar da rahoton bacewarsu a ranar Larabar da ta gabata bayan wata ambaliyar ruwa da ta afku a jihar Sikkim da ke Arewa maso Gabashin kasar, kamar yadda mai magana da yawun rundunar tsaron ya bayyana.

 

Ruwan sama ya mamaye wani kwari mai tazarar kilomita 150 daga arewacin Gangtok, babban birnin jihar, dake kan iyaka da kasar Sin.

 

“Wasu runfunan Sojoji da ke cikin kwarin ya shafa kuma ana kokarin tabbatar da cikakken bayani,” in ji Kakakin da ke birnin Guwahati.

 

Kakakin ya kara da cewa, tashin ruwa ya nutsar da wasu motoci biyo bayan fitar da ruwa daga dam.

 

Ruwan sama na tsaka-tsaki da tsawa na kawo cikas ga ayyukan ceto a yankin, in ji wani jami’in Sojin da ya nemi a sakaya sunansa.

 

 

 

REUTERS

Ladan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *