Take a fresh look at your lifestyle.

APC Ta Dakatar Da Yakin Neman Zaben Gwamnan Jihar Kogi

0 110

Jam’iyyar All Progressives Congress, APC ta dakatar da yakin neman zaben gwamnan jihar Kogi da za a yi ranar 11 ga watan Nuwamba.

 

Jam’iyyar ta ce ta dauki matakin ne domin nuna girmamawa ga Ms Khadijat Yahaya, ‘yar jam’iyyar da ta mutu bayan wani hari da wasu da ake zargin ‘yan daba ne suka kai musu.

 

Kakakin Majalisar Kamfen na jihar, Mista Kingsley Fanwo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Lokoja, babban birnin jihar.

 

Ana zargin Khadijat ta rasa ranta ne bayan wani rikici tsakanin magoya bayan jam’iyyar Social Democratic Party, SDP da na APC a Kotonkarfe a ranar 29 ga watan Satumba.

 

A halin da ake ciki, dan takarar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar APC, Alhaji Usman Ododo, ya ziyarci iyalan marigayiyar a Kotonkarfe a ranar Talata domin jajanta musu bisa rasuwar ta.

 

Ododo ta bayyana kaduwarsa da rasuwar ta, sannan ta yi addu’ar Allah ya jikan ta.

 

Da yake mayar da martani, Malam Saliu Akawu, ya gode wa Ododo bisa wannan ziyarar.

 

Akawu ya ce halin da Ododo ya yi ya nuna cewa shi shugaba ne mai tausayin jama’ar sa.

 

Ya ce Khadijat mutuniyar ce mai son zaman lafiya wacce miyagun mutane suka yanke rayuwarta.

 

Ododo ya kuma ziyarci fadar Ohimege na Kotonkarfe, Alhaji Abdulrazak Koto, inda ya nuna alhininsa kan rasuwar Khadijat.

 

Ya bayyana ta a matsayin mace mai son zaman lafiya mai son ganin cigaba a Kotonkarfe tare da alkawarin tabbatar da adalci ga iyalan mamacin.

 

 

 

NAN/Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *