Take a fresh look at your lifestyle.

Harin Jiragen Sama: Siriya Ta Yi Zaman Makoki Da Jimamen Wadanda Aka Kashe A Homs

2 143

‘Yan kasar Syria sun fara binne gomman mutanen da suka mutu a wani harin da jiragen yaki mara matuki suka kai a makarantar horas da sojoji da ke yammacin birnin Homs.

 

Akwatunan gawa da aka lullube da tutocin Syria a ranar Juma’a sun yi jerin gwano a kan titunan wajen asibitin sojoji na Homs.

 

A ranar alhamis din da ta gabata wasu jiragen marasa matuka sun kai hari a wajen bikin yaye dalibai a farfajiyar makarantar, inda iyalai suka taru tare da sabbin jami’an.

 

Ma’aikatar lafiya ta Syria ta ce akalla mutane 89 ne suka mutu, ciki har da mata 31 da kananan yara biyar.

 

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Syria da ke sa ido kan rikicin na Syria ta ce adadin mutanen ya haura 120.

 

Syria ta ayyana kwanaki uku na zaman makoki na kasa.

 

Kawo yanzu dai babu wani ikirarin daukar alhakin kai harin.

 

 

 

ALJAZEERA/Ladan Nasidi.

2 responses to “Harin Jiragen Sama: Siriya Ta Yi Zaman Makoki Da Jimamen Wadanda Aka Kashe A Homs”

  1. саптық және жорықтық адым, саптық адым тасбих электронный не айту керек, тасбих тарту не
    айту керек шәкірт жетістігі
    мұғалімнің кәсіби біліктілігі мен шеберлігінің жемісі, шәкірт деген не химия 9 сынып бжб 1 тоқсан, химия 9 сынып бжб 2 2 тоқсан

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *