Take a fresh look at your lifestyle.

GWAMNA ZULUM YA RABAR DA KAYAYYAKIN MASARUFI GA AL’UMAR BAMA

TIJJANI USMAN BELLO

0 127

Gwamnan jihar Barno,dake Arewa mao gabashin Najeriya,Farfesa Babagana Umara Zulum,ya kai ziyarar aiki ta wuni uku a karamar hukumar Bama domin tallafa wa al;umar yankin dake cikin halin kakani kayi, yace:” Biyo bayan Kaddamar da shirin bayar da Tallafi Jin Kai da Walwalar Al’umma, wanda Shugaba Buhari ya yi a ranar Jin Kai da Walwalar Al’umma ta Duniya a nan garin Maiduguri, ya sanyamu bin wannan turba duk da cewar dama dai muna yin dai–dai gwargwadon Karfinmu.”

 

’’wannan Lokacin mun lura da cewar Yankin Karamar Hukumar Bama na daya daga cikin Yankunan da suka sha fama tare da Wahalar Boko Haram a shekarun bayannan na Rashin Muhalli, Abinci, da Kayayykin More Rayuwa ta yadda a yanzu haka alumman garin da kuma ita kanta garin na matsanancin bukatar taimako cikin gaggawa don tallafawa kowa da nufin samun saukin gudanar da Rayuwa’’a cewar Gwamna.

 

 

“Abunda yasa muka mayar da hankalinmu wajen inganta rayuwar al’umma don samun saukin rayuwa, da hakane muke mika Wadannan Kayayykin Abinci da Tufafi ga Mata, har na Naira Miliyan Dari Hudu, ga Mabukata har Dubu 90.”

 

Haka zalika Gwamnan, ya yi irin wannan rabon ga Kungiyoyin Sa Kai na Mayakan da suke taimakawa Jami’an Tsaron irin su Kungiyoyin Maharba da na CJTF,  da Vigilante, gami kuma da  Kungiyar Tsaron Kan Iyaka mai Suna Kesh–Kesh, da yawansu ya kai  Kusa da Dubu Daya, da Kayayykin Abinci na sama da Naira Miliyan Dubu 14.5.

 

Gwamnan Har ila yau, ya bayar da Umarnin gyara Bubban Asibitin Kwararru dake garin Baman cikin gaggawa tare da Daukan Likitoci da Ma’aikatan Jinya da Unguwar Zoma, har sama da 30.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *