Take a fresh look at your lifestyle.

Iran Ta Yi Kira Ga Kasashen Musulmi Da Su Kakaba Wa Isra’ila Takunkumi

0 142

Ministan harkokin wajen Iran Hossein Amirabdollahian ya bayyana a jiya Laraba cewa, ya kamata mambobin kungiyar hadin kan kasashen musulmi OIC su kakaba wa Isra’ila takunkumin hana man fetur da sauran takunkumai, tare da korar dukkanin jakadun Isra’ila.

 

Ana gudanar da wani taron gaggawa na kungiyar OIC a birnin Jeddah na kasar Saudiyya domin tattauna rikicin da ke ci gaba da ruruwa tsakanin Isra’ila da Falasdinu, bayan wani harin bam da aka kai a wani asibitin Gaza da yammacin ranar Talata wanda ya yi sanadiyar mutuwar dimbin Falasdinawa.

 

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa: “Ministan harkokin wajen kasar ya yi kira da a gaggauta sanyawa Isra’ila cikakken takunkumi daga kasashen musulmi, gami da takunkumin mai, baya ga korar jakadun Isra’ila idan har aka kulla alaka da gwamnatin yahudawa.”

 

Amirabdollahian ya kuma yi kira da a kafa wata tawaga ta lauyoyin Musulunci da za ta rubuta laifukan yaki da Isra’ila ta aikata a Gaza.

 

Gabanin fashewar wani abu a asibitin Gaza a ranar Talata, Hukumomin lafiya a Gaza sun ce akalla mutane 3,000 ne suka mutu a harin bam na kwanaki 11 da Isra’ila ta yi bayan harin ba-zata da Hamas ta kai.

 

 

 

REUTERS/ Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *