Take a fresh look at your lifestyle.

Oyetola Ya Taya Shugaba Tinubu Murnar Nasarar Kotun Koli

0 102

Ministan Ma’aikatar Ruwa da Tattalin Arzikin Ruwa, Adegboyega Oyetola ya taya Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima da kuma Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje murnar nasarar da suka samu a Kotun Koli.

 

 

Ya kuma yi kira ga ‘yan adawa da su hada kai da shugaban kasa domin gina kasa.

 

 

Oyetola ya bayyana hukuncin a matsayin “mai kyau” wanda zai kara zurfafa dokokin zaben kasar da kuma hukumcin shari’a.

 

 

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa Ismail Omipidan ya fitar, Oyetola ya ce hukuncin da kotun kolin ta yanke ya kawo karshen takaddamar da ake yi a zaben shugaban kasa na 2023, yana mai cewa dole ne masoya dimokuradiyya su yaba da tsayin dakan da bangaren shari’a suka yi wajen zurfafa dimokuradiyyar kasar nan ta hanyar sahihiyar hukumci.

 

 

“A madadin iyalan APC na Osun, ina taya shugaban mu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima murnar nasarar da suka samu a kotun koli.

 

“Hukuncin yau ya kawo karshen cece-ku-ce, ruguzawa, da kararrakin da aka yi wa zaben shugaban kasa na 2023. Ina fata ‘yan adawa za su hada kai da shugaban kasar mu domin ciyar da Najeriya gaba domin moriyar kasar baki daya,” inji Oyetola.

 

 

Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *