Majalisar Dinkin Duniya ta ce Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango a halin yanzu tana da mutane miliyan 6.9 da suka rasa matsugunan su sakamakon karuwar tashe-tashen hankula.
Hukumar Kula da Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta tattara bayanan bin diddigin daga dukkan larduna 26 na kasar. Ta ce akasarin wadanda suka rasa matsugunansu na zaune ne a gabas inda aka ce rikici ne ya haddasa.
A arewacin Kivu kadai, a bana mutane kusan miliyan daya ne suka tsere daga gidajensu, sakamakon yakin da ake yi da ‘yan tawayen M23.
Ta yi gargadin cewa DR Congo na fuskantar daya daga cikin manyan matsalolin gudun hijira da rikicin jin kai a duniya.
BBC/ Ladan Nasidi.
Leave a Reply