ILRTI Ta Nemi Hadin Kan Masu Ruwa DaTsaki A Kokarin Magance Matsalar Tsaro Da Abinci A Najeriya.
Abdulkarim Rabiu, Abuja
Cibiyar Nazari da Bada Horo a kan Kiwon Dabbobi ta Kasa da Kasa wato International Livestock Research and Training Institute (ILRTI) ta bukaci hadin kan masu ruwa da tsaki domin magance matsalar abinci da samar da ingantaccen kiwo da noma da kuma tsaro a Najeriya.
Shugaban cibiyar Dakta Kabir Dasuki shi ne ya bukaci hakan a wani taron maneme labarai da cibiyar ta shirya tare da hadin gwiwar kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah Cattle Breeders Association Of Nigeria ranar Talatar nan a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.
Da yake gabatar da jawabi a taron Dr Kabir Dasuki ya ce kiwon daddobi na da mutukar mahinmanci a Najeriya saboda irin gudunmawar da yake bayarwa a bangaren tattalin arziki da samar da ayyukan yi a kasar.
Ya ce an kafa wannan cibiya ce da nufin samar da abinci mai gina jiki da tsaron kasa wanda hakan zai taikmaka wajen rage talauci da inganta kiwon kafiya da samar da ayyukan yi sannan za a kuma a iya fitar da dabbobin zuwa kasashen waje.
To sai dai ya ce matsalar tsaro da ayyukan ta’adanci dake addabar wasu sassan arewacin kasar na mutukar yin barazana ga kiwon dabbobin, a dalilin hakan ne ya sa cibiyar ta kudiri aniyyar yin dukkan maiyuwa domin ganin an kawo karshe matsalar.
“mun kira masana , mun zauna da turawa da mutane wadanda suka san kan harkar kiwon dabbobi sannan mun fitar da jadawali kan yadda za a magance wannnan matsalar, shi ya sa muka bullo da wannan tsari” In ji Dakta Kabir Dasuki
Ya ce kungiyar za ta rika bada hoto na dabarun kiwon dabbobi tare da samar da iri da kuma nunawa wadanda suka samu horon hanyoyin da za su sayar da dabbobin da suka kiwata.
Shi kuwa shugaban kungiyar Fulani makiyaya ta kasa Ta Miyeeti Allah Kettle Breeders Association of Najeriya, MACBAN, Baba Usman Ngenzarma, ya bayyana cewa za su baiwa cibiyar hadin kai dari bisa dari domin anfanin Fulani makiyaya da ma Najeriya baki daya.
“Duk wata harka irin wannan na ci gaba idan ta zo ai bamu da wani tunani illa mukarbe ta, mu ga tayya zai taimakawa fulani makiyaya don futo da su daga hali na kaka na kayi da suke ciki, Don haka muna maraba da wannan shiri” In ji shugaban na Miyetti Allah
Shi ma Maitaimakin shugaban kungiyar Tabital Pulaako ta kasa da kasa, Auwal Abubakar Gonga ya ce za su bada gudunmawarsu ta hanyar wayar da kan al’ummar Fulani a game da wannan tsari domin su amfana da horon da cibiyar ke bayarwa
“Dolene mu hada kai mu wayar da kansu kuma mu nuna musu yadda za a yi kiwon na zamani sannan mu ja kunnensu, su guji shiga ayyukan bata gari” In ji Auwal Gonga
Daga karshe Cibiyar ta ILRTL ta nemi hadin kan dukkan masu ruwa da tsaki su mara mata baya a wannan tafiyar don cimma burinsu na bada horon kan dabarun kiwon dabbobi na zamani, da wadata kasa da abinci, da samar da ayyukan yi, da kuma bunkasa tattalin arziki.
Taron na hadin gwiwa tsakanin cibiyar ILRTI da kungiyar Miyetti Allah (MACBAN) da Fulbe Global Development and Right Initiative ya samu halartar wakilan kungiyoyin makiyaya daban-daban dake Najeriya da kuma masu ruwa da tsaki a fannin kiwo da ma yan jaridu dake ciki da wajen Najeriya.
Abdulkarim Rabiu
Fantastic material. Cheers.
how to choose an online casino https://casinoslotoking.com/betwhale/ online casino slots of vegas
Terrific stuff, Thank you!
casino canada online https://combatcasino.info/michigan-online-casinos/ online casino worth it