Shugaba Tinubu ya ayyana bude taron shekara-shekara karo na 43 da kuma na 18th Manajan Daraktar Kungiyar gudanar da Mulkin Tashar Jirgin Ruwa ta Yammaci da Tsakiyar Afirka (PMAWCA).
Shugaban wanda ya samu wakilcin ministan harkokin jiragen ruwa da tattalin arzikin ruwa, Adegboyega Oyetola, shugaban ya bukaci kasashen Afirka da su hada kai don amfanin yankin tun da dai bangaren teku ba wai kawai ya kasance cibiyar samar da kasuwanci ba ne, har ma da dunkulewar Nahiyar Afirka baki daya.
Ya ci gaba da cewa, a matsayin shi na gwamnati, ya yi imanin cewa, ya wajaba a sanya fasahar sadarwa a cikin harkokin gudanarwar jama’a, domin taimakawa wajen tabbatar da gaskiya da kuma saukaka harkokin kasuwanci, yana mai cewa, “gwamnati tana baiwa hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Nijeriya duk wani goyon baya da ya dace don ganin an gaggauta aiwatar da ayyukan al’ummar tashar jiragen ruwa. Tsarin wanda shine mafarin aiwatar da Tagar Single ta Kasa.”
A cewar shi, “an gamsu da cewa cikakken sarrafa kan shi ita ce hanya daya tilo da za mu bi idan muka shirya ci gaba da yin gasa a masana’antar ruwa ta duniya.”
A gefe guda kuma, kafin gabatar da jawabin shugaban, ministan ya nanata bukatar gyara da sake gina tashoshin jiragen ruwa da ake da su a inda ya dace.
President Tinubu declares open 43rd PMAWCA conference
President Tinubu, today , declared open the 43rd Annual Conference and 18th Managing Director’s Roundtable of the Port Management Association of West and Central Africa (PMAWCA).
Represented by the minister of Marine and… pic.twitter.com/FB8DdKiZl5
— Imran Muhammad (@Imranmuhdz) November 6, 2023
Ladan Nasidi.
Leave a Reply