Take a fresh look at your lifestyle.

Hukunta Masu Laifi Domin Hana Sake Faruwar Hakan: Bello Bodejo

By Nura Muhammad

0 390

An bukaci Gwamnatin Jihar Neja dake arewa ta tsakiyar Najeriya da ta binciki rikicin da yayi sanadiyar yanke hannayen yaron Fulani dake kiwo a karamar hukumar Lapai dake jihar.

Shugaban Kungiyar Miyatti Allah Kautal Hore ta Kasa Alhaji Bello Bodejo shine ya bukaci hakan a zantawar sa da manema labarai a garin Lapai Jim kadan bayan ya ziyarci yaron a babban Asibin Karamar hukumar ta Lapai.

Shugaban ya ce hukuncin da aka dauka kan yaran mai suna Bello Mohammed dan shekaru 10 da hauhuwa na rashin imanine , a don haka ya bukaci hukumomin da su bincika kana su hukunta duk wanda aka samu da hannu a cikin aika aikar domin kaucewa sake aikata irin haka a nan gaba

Alhaji Bello Bodejo ya ce ya zo karamar hukumar Lapai ne domin ganema Idon sa irin barnar da aka yiwa yaron da bai ji bai gani ba, kawai saboda son zuciya da kuma rashin Imani, da Kuma kawo rashin lafiya a tsakankanin alumma.

Ya kara da cewar ba Shari’ar, da ta ce a dau irin wannan danyen hukuncin kan yaro dan shekara 10 dake aikin kiwo don neman rufin asiri ga iyayen sa.

Tun da dai ba Shari’ar musulunci ake bayi ba ta Yaya za a yankewa yaron hannu ba laifin fari ko na Baki, a don haka dole ne a Nemo da Kuma hukunta wadanda suka aikata wannan aika aikan.” Bello Bodejo

Ya kuma ce kungiyar ta Miyatti Allah kautal Hore da gwamnatin jihar Neja nan gaba kadan zasu hadu domin tattauna yadda za a lalibo bakin zaran na ganin an kawo karshen matsalar rikici tsakanin Fulani da manoma.

Shugaban kungiyar ya Kara da cewar, bayan ganawa da Shugabanin kungiyar ta kautal Hore da kuma DPO yan sanda na karamar hukumar Lapai ya samu tabbacin cewar hukumomi tsaro na iyakar kokarin su na ganin an magance matsalar da kuma hukunta duk wanda aka samu da hannu cikin lamarin.

A kwanaki baya ne dai wasu da ake kyautata zaton manoma ne suka kama da kuma yankewa Bello Mohammed dan shekara 10 da hauhuwa hannu sakamakon suna zargin sa da shiga gonar su lamarin da ya kawo tada jijiyoyin wuya, inda tuni gwamnatin Jihar ta Yi Allawadai da danyan aikin, ta kuma aha alwashin hukunta duk wanda aka samu da laifin.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *