An kewaye wasu asibitoci da dama kuma an kashe akalla mutane uku a yayin da sojojin Isra’ila suka kaddamar da wani gagarumin farmaki kan Jenin a yammacin gabar kogin Jordan da suka mamaye.
Hare-haren da aka kaddamar da daddare kuma har zuwa ranar Juma’a, sun kuma jikkata wasu akalla 14 a cewar majiyoyin Falasdinawa. An kawo karshen farmakin bayan sa’o’i da dama.
Wani harin da jirgin sama mara matuki ya kai a sansanin ‘yan gudun hijira na Jenin ya kashe akalla mutane uku, in ji ma’aikatar daukar marasa lafiya ta Falasdinu, amma rundunar sojin Isra’ila ta ce biyar ne suka mutu. Ana ci gaba da kai hare-hare ta sama a yammacin gabar kogin Jordan yayin da yakin Gaza ke kara kamari.
Kamfanin dillancin labaran kasar Falasdinu Wafa ya bayar da rahoton cewa, Sojojin Isra’ila sun hana ayyukan agajin gaggawa isa ga wadanda suka jikkata, lamarin da ka iya jefa rayuka cikin hadari.
Tun da misalin karfe 10:30 na daren jiya alhamis, sojojin Isra’ila sun tura akalla motocin soji 80 cikin birnin Jenin, inda suka kai farmaki gidajen Falasdinawa tare da tsare mutane da dama. An samu rahotannin tashin hankali.
“Motoci masu sulke da dama ne suka taru, tare da buldoza suma, suna lalata motoci, suna lalata hanyoyi,” in ji Sara Khairat ta Aljazeera daga mamayar Gabashin Jerusalem. An kwashe kimanin awanni takwas ana kai samamen.
Akalla asibitoci hudu ne sojojin Isra’ila suka kewaye ciki har da asibitin Ibn Sina.
Sojojin Isra’ila sun kai hari a asibitin Ibn Sina, daya daga cikin mafi girma a yammacin gabar kogin Jordan da suka mamaye. Sun kai farmaki inda suka nemi ma’aikatan lafiya da su sa hannu su fice daga asibitin.” Inji Khairat.
Likitoci da dama daga asibitin sun ki bin umarnin tare da kwashe su; Ta kara da cewa an kama ma’aikatan lafiya biyu.
“Yana da mahimmanci a lura cewa wannan ya faru ne a sansanin ‘yan gudun hijira na Jenin, inda kusan kullun ke tashe-tashen hankula… Ba wai asibiti kadai ba, amma yadda sojojin Isra’ila ke shigowa,” Khairat ta ci gaba da cewa.
Tun bayan da Isra’ila ta kaddamar da yakin Hamas a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 11,500 a zirin Gaza.
Dakarun Isra’ila sun kama Falasdinawa 47 a Yammacin Gabar Kogin Jordan a cikin dare, in ji Hukumar Kula da Fursunoni da Tsoffin Fursunoni a ranar Juma’a. 26 daga cikin mutanen da aka kama suna Nelin da ke yammacin Ramallah.
A wani shingen binciken ababan hawa da ke arewacin Hebron, an yi artabu tsakanin mayakan Falasdinawa da sojojin Isra’ila a ranar Juma’a, inda aka kashe Falasdinawa biyu, in ji Zein Basravi na Aljazeera, wanda ya ruwaito daga Ramallah.
A ranar alhamis din da ta gabata ne sojojin Isra’ila suka harbe wasu Falasdinawa uku bayan da suka bude wuta a wani shingen binciken ababan hawa da ke gabar yammacin kogin Jordan. Sojan Isra’ila daya ya mutu a wannan harin, a cewar jami’an Isra’ila.
Basravi ya ce irin wadannan hare-hare ta hanyar amfani da kananan makamai da bama-bamai sun karu a cikin ‘yan makonnin da suka gabata a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna bacin ransu kan mutuwar fararen hula a Gaza da kuma mamayar yammacin gabar kogin Jordan.
Ya ce, “Yayin da Isra’ila ke ci gaba da zafafa zafi, tana mai da martani ga al’ummar Falasdinu, mutane sun fara ja da baya,” in ji shi.
Tun a ranar 7 ga watan Oktoba aka kashe Falasdinawa 203 a hare-haren da Isra’ila ta kai a yammacin gabar kogin Jordan.
ALJAZEERA/Ladan Nasidi.
тостер купить, тостер цена сулпак rub courses, course of dollar
машина времени жастар, купить билеты на машину
времени бала сөзін тәуелдеу, білім сөзін тәуелдеу
совместимость знаков зодиака в любви стрелец мужчина и овен мужчина полутень заговор в суде текст никколо макиавелли цитаты, макиавелли цитаты о политике
сонник гадалка нагадала детей магическое истощение это
подработка на выходные домодедово с ежедневной вакансии швеи в новосибирске на подработку
подработка в новосергиевка работа на подработку ижевск