Kasashe biyar na Turai da Canada sun hada kai don shiga cikin shari’ar kisan kiyashi da kotun kasa da kasa ta ICJ ke tuhumar Myanmar da aikatawa al’ummar Rohingya.
Kotun koli ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce Denmark, Faransa, Jamus, Netherlands da Biritaniya sun gabatar da sanarwar shiga tsakani a cikin karar da Gambia ta shigar a shekarar 2019.
Kungiyar ta ba da misali da “sha’awar gama gari don cim ma manyan manufofi” na yarjejeniyar 1948 kan rigakafi da hukunta kisan kiyashi.
“Muna son bayar da gudumawa don fayyace da kuma yaki da kisan kiyashi. Muna mai da hankali musamman kan cin zarafin mata da yara, ” Tania von Uslar, Darakta-Janar na Hulda da Shari’a ta Jamus ta fada a cikin wata sanarwa ta X.
Kotun ta ce kasar Maldives ta gabatar da wata sanarwa ta daban tana zargin Myanmar da aikata kisan kiyashi.
A karkashin dokokin ICJ, sanarwar na nufin wadannan kasashe za su iya ba da hujjar shari’a a shari’ar da aka gabatar a shekarar 2019 bayan fusatar da kasashen duniya suka yi kan al’ummar musulmi ‘yan tsiraru na Rohingya.
Tawagar binciken gaskiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta kammala da cewa yakin sojin Myanmar na 2017 wanda ya kori ‘yan Rohingya 730,000 zuwa Bangladesh makwabciyarta ya hada da “ayyukan kisan kare dangi”.
Myanmar ta musanta kisan kiyashi, inda ta yi watsi da binciken da Majalisar Dinkin Duniya ta yi a matsayin “mai son zuciya da kuma kurakurai”. Ta ce ta na murkushe ‘yan tawayen Rohingya ne da suka kai hare-hare.
Sai dai kotun ta ICJ ta yi watsi da kin amincewar Myanmar kan shari’ar kisan kiyashin da aka yi a watan Yulin bara, wanda hakan ya ba da damar sauraron karar gaba daya.
ALJAZEERA/Ladan Nasidi.
Leave a Reply